Kwankwaso ya isa Kano bayan komawarsa jam’iyyar NDC

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya sauka a Kano a safiyar Litinin, sa’o’i kaɗan bayan sanar da komawarsa jam’iyyar NDC.

Rahotanni sun nuna cewa magoya bayansa da dama sun tarbe shi a filin jirgin sama tare da nuna farin ciki da goyon baya bayan sauyin jam’iyyar.

Komawar Kwankwaso zuwa jam’iyyar NDC na zuwa ne a daidai lokacin da harkokin siyasa ke ƙara ɗaukar zafi gabanin zaɓukan 2027, lamarin da ke ci gaba da jawo martani daga bangarori daban-daban na siyasa.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu cikakken bayani daga Kwankwaso kan matakan da zai ɗauka a sabuwar jam’iyyarsa.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

Exit mobile version