Kotun Tarayya Ta Wanke Abba Kyari

A ranar Alhamis, wata Kotun Tarayya a Abuja ta wanke Abba Kyari, wanda aka dakatar a matsayin Mataimakin Kwamishinan Yan Sanda daga zargin bayar da bayanin dukiya mai lissafin 23 da Hukumar Kula da Laifukan Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta shigar da shi.

Mai shari’a James Omotosho ya bayyana a cikin hukuncin cewa, masu shigar da kara ba su iya tabbatar da zarge-zargen da aka kawo wa Kyari da sauran wadanda ake kara a shari’ar ba.

NDLEA ta zargi jami’in yan sandan da aka dakatar da kasa yin bayanin wasu kadarori, sannan ta shigar da shi tare da yan,uwansa, Mohammed Kyari da Ali Kyari. Hukumar ta ce ‘yan uwansu sun rika bayar da takardun shaidar bogi domin boye asalin wasu kadarori da ake zargin suna da alaka da jami’in yan sandan.

Sai dai, Mai Shari’a Omotosho ya ce hukumar NDLEA ba ta gabatar da hujjoji masu karfi da za su nuna cewa kadarorin da ke cikin zarge-zargen mallakar Kyari ne ba.

Alkalin ya kara da cewa, mallakar kasa da dukiya tana bukatar a nuna ta, ta hanyar hujjojin doka da ake yarda da su kamar tarihin gargajiya, takardun mallaka na doka, ayyukan rike dukiya, ko wasu hujjojin da ke danganta mutum kai tsaye da kadarar.

Ya ce masu shigar da kara ba su gabatar da irin waɗannan hujjoji ba don nuna cewa wani gida dake Fountain Estate, wanda aka ce na Ramatu Kyari ne, mallakar jami’in yan sandan da aka dakatar ne.

Kotun ta kuma gano cewa NDLEA ba ta iya kawo hujja mai karfi da ke danganta Kyari da sauran kadarorin da aka ambata a cikin zargin ba, ciki har da gine-gine a Linda Choko Road, Asokoro, Abuja da wani gida a Maiduguri, Jihar Borno.

A lokacin shari’ar, Kyari ya bayyana wa kotun cewa gidan Maiduguri na marigayin mahaifinsa ne, kuma ya gaji shi tare da ‘yan uwansa. Mai shari’a Omotosho ya lura cewa masu shigar da kara ba su musanta wannan hujja ba.

Alkalin ya kuma yi watsi da zarge-zargen hada-hadar da aka yi wa ‘yan uwa Kyari, inda ya ce babu wata hujja da ta nuna cewa sun bayar da takardun bogi domin ɓoye mallakar dukiya.

Mai shari’a Omotosho ya bayyana cewa shari’ar masu shigar da kara ba ta da karfi kuma ba ta da hujjojin da za a iya dogara da su, ya kara da cewa Kyari ya yi hidima ga kasa kuma ba za a tilasta masa wahala ba a rashin shaidar da ta gamsar.

Duk da wannan wankewar a shari’ar bayanin dukiya, Kyari da wasu jami’an yan sanda hudu da aka dakatar suna ci gaba da fuskantar wata shari’a daban a gaban Mai Shari’a Emeka Nwite kan zargin hannu a harkar safarar kwayar cocaine.

An riga an yanke wa wasu mutane biyu da ake zargin suna safarar kwaya da wannan al’amari ke da alaka da su, Chibunna Patrick Umeibe da Emeka Alphonsus Ezenwanne, hukunci na shekaru biyu a gidan yari a shekarar 2022.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.
Exit mobile version