A yau ne mai girma Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya karbi fom na takarar kujerar shugaban ƙasar Nijeriya a shekarar 2023 tare da tabbacin cewa-: idan aka ba shi dama tabbas zai zama shugaba na kowa da kowa ba tare da nuna wani bambanci ba.
Gwamna Bala ya furta hakan ne yau a birnin tarayya Abuja lokacin da yake magana yayin da wasu kungiyoyin matasan Najeriya karkashin jagorancin GBAM suka sai masa fom din takarar kujerar shugaban ƙasar Nijeriya a zaben 2023.
A cewar Gwamnan idan Ubangiji ya tabbatar masa da nasara to kuwa gwamnatinsa za ta zamo Gwamnati ce mai tabbatar da a hadin kai da kaunar juna tsakanin Yan Nijeriya.
Gwamnan yace Gwamnati sa zata kasance ne ta dukkan yan kasa da zata kau da bambance ban bance tsakanin yan Nijeriya.
Kuma gwamnati ce da za tayi aiki tukuru don ganin ‘yan kasa daga lungu da sakon Nijeriya sun ci gajiyar gwamnatin tarayya ba tare da nuna bambanci ba.
Gwamnan ya yabawa kungiyar BAM bisa wannan karimcin, da sukayi masa domin nuna kauna da karfin gwiwa da kuma yi masa kyaukyawar sheda a matsayin mutum da zai iya shugaban cin kasa kamar Nijeriya.
Gwamnan yace kungiyar matasa ne ke jagorancin ta wanda hakan ya kara masa kaimi wajen ganin ya samar wa matasa dukkan abinda ya kamata domin inganta rayuwar su.
Gwamna Bala Mohammed ya ce zai tabbatar da cewa matasa da mata ab dama dasu ta ko wacce fanni a Gwamnatin sa idan Allah ya nufa an kai ga Nasara.
Gwamnan ya bayyana jam’iyyar su ta PDP a matsayin jam’iyyar siyasa mafi karfi kuma babbar jam’iyyar siyasa a nahiyar Afirka, wanda take da tsari da kyawawan shirye shirye da zata iya kai Nijeriya Tudun mun tsira.
Bala Mohammed ya kara da cewa zai kasance mai gaskiya da riƙon amana yayin gudanar da shugaban cin Nijeriya idan ya kai ga nasara.
Gwamnan yace Baiyi mamaki da irin wannan karamci da matasa suka masa ba domin kuwa su mutane ne da suke da fikra kan abinda zai amfani Kasar su.
Fatana kawai Ubangiji Allah ya bamu ikon cika musu burin su na ganin sabuwar Nijeriya da zata inganta rayuwar su.
A karshe yayi Gwamnan ya gabatar da Godiya ta musamman ga kungiyar magoya bayan sa ta (BAM-V) karkashin jagorancin kodinetan ta na kasa Kwamared Jibo Muhammad tare da yin alkawarin ci gaba da bullo da tsare-tsare da nufin inganta rayuwar ‘yan Najeriya baki daya.
A nasa jawabin na Godiya shugaban jam’iyyar PDP na jihar Bauchi Alhaji Hamza Koshe Akuyam ya yaba da yadda kungiyar ta (BAM-V) suka ta fafutukan su daki daki har kawo wannan lokaci da suka gabatar da fom na takarar kujerar shugaban ƙasar Nijeriya ga Gwamna Bala Abdulkadir.
Koshe Akuyam ya tabbatar musu da cewa ko shakka bayi yi kan cewa Gwamna Bala Abdulkadir zai zamo ma Yan Nijeriya alheri mai girma idan ya samo shugaban kasa domin akwai alheri a tattare da shi ga Dukkanin wanda ya San shi. Ko shakka ba nayi zai zame ma Yan Nijeriya abin alfahari.
Lawal Muazu Bauchi: Mai Taimakawa Gwamnan Bauchi kan Sabbin Kafafen Yada Labarai na zamani 24/03/22