A safiyar jiya Laraba, wani labari mai tada hankali ya faru a yankin Gwagwalada, Abuja, inda wani mutum mai suna Lawal Ibrahim ya mutu a ɗakin otal yayin fasikanci da wata matashiya mai suna Maryam Abba, ’yar birnin Dutse, jihar Jigawa. Wannan labari ya jawo cece-kuce, inda ake ganin darasi mai tsanani ga matasa da ke aikata abubuwa na fasadi.
Mun samu labari a shafin Datti Assalafiy yana cewa Bayan shafe watanni uku suna mu’amala a shafin sada zumunta, Lawal Ibrahim ya kira Maryam zuwa Abuja. Ya sauke ta a wani otal mai suna Palasa Hotel a jiya da daddare, inda suka kwana tare. Da asubahin yau da misalin ƙarfe 6:00 na safe, Maryam ta bayyana cewa suna cikin yin zina ne sai Lawal ya faɗo daga kanta ya suma. Ta yi ƙoƙarin yayyafa masa ruwa don farfaɗowa, amma abin ya gagara.
Bayan haka, Maryam ta sanar da ma’aikatan otal ɗin, inda aka garzaya da Lawal asibiti. Likitoci sun tabbatar cewa ya mutu. Wannan ne ya sa manajan otal ɗin ya kai ƙara ofishin ’yan sanda na Gwagwalada.
A yanzu haka, Maryam tana hannun jami’an tsaro, inda aka tafi da ita Force CID Abuja domin ci gaba da bincike kan musabbabin mutuwar Lawal. Abubuwan da aka gano a ɗakin otal ɗin sun haɗa da kankana da miyagun ƙwayoyi masu ƙara ƙarfin jima’i.