Mutane da dama a Israel sun jikkata bayan wani harin makami mai linzami da Iran ta harba, wanda ya fada wani kauye da ke arewacin kasar a safiyar Juma’a, kamar yadda hukumomin agajin gaggawa suka bayyana.
A cewar hukumar agajin gaggawa ta Magen David Adom, jami’an jinya sun yi wa mutum 58 da suka jikkata magani tare da kai su asibitocin yankin bayan harin da ya auku a garin Zarzir kusa da Nazareth.
Rahotannin kafofin watsa labaran Isra’ila sun ce wata mata ta samu mummunan rauni sakamakon gutsattsarin ƙarfen roka, kuma har yanzu halin da take ciki bai tabbata ba.
Rundunar sojin Israel Defense Forces ta bayyana cewa ta tura wata tawagar sojoji zuwa wurin da harin ya faru.
A cikin wata sanarwa, rundunar ta ce jami’anta tare da hukumomin agaji da na ceto suna ci gaba da duba halin da ake ciki a yankin.
A ranar Alhamis ma, ma’aikatar lafiya ta Isra’ila ta ce adadin mutanen da suka jikkata sakamakon hare-haren makamai masu linzami da Iran ke kai wa ƙasar ya kai mutane 2,745.
