Isra’ila Ta Yi Gargadi Kan Farautar Mai Gado Jagorancin Addinin Iran

Rundunar sojin Isra’ila ta yi gargadi cewa za ta ci gaba da farautar duk wanda ya gaji matsayin jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei.

A wani sako da rundunar ta wallafa a shafinta na X, rundunar ta bayyana cewa: “Mun samu bayanin cewa nan ba da jimawa ba, Majalisar Manyan Malaman Iran, wadda ba ta yi zama ba tsawon shekaru, za ta yi taro a birnin Qom don zaɓar sabon jagora.”

Rundunar ta kara da cewa: “Muna so mu bayyana wa majalisar cewa Isra’ila za ta ci gaba da farautar duk wanda ya gaji matsayin jagoran addinin ƙasar da kuma duk mutumin da ya nemi wannan mukami.”

Ta kuma yi gargadin cewa: “Ga duk wadanda ke shirin halartar wannan taro, ba abin da zai hana mu kai musu hari. Wannan gargadi ne a fili.”

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.
Exit mobile version