Rahotanni daga wasu kafofin watsa labarai sun bayyana cewa gwamnatin Isra’ila ta cire sunan Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Aragchi, daga jerin mutanen da ake zargin tana shirin kai wa hari.
Rahotannin sun kuma nuna cewa an cire sunan Kakakin Majalisar Dokokin Iran, Mohammad Baqer Qalibaf, daga wannan jerin bayan wasu ƙasashe sun shiga tsakani.
Wata majiyar tsaro daga ƙasar Pakistan ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa jami’an Pakistan tare da wasu daga Amurka sun buƙaci Isra’ila da ta janye wannan shiri, domin kauce wa rikicin da ka iya dagula yunƙurin da ake yi na samar da zaman lafiya a yankin.
Majiyar ta bayyana cewa duk wani hari da zai shafi manyan jami’an Iran na iya kawo cikas ga tattaunawar diflomasiyya da ake yi domin rage tashin hankali tsakanin ƙasashen.
Haka kuma wasu kafofin yaɗa labarai na Amurka sun ruwaito irin wannan bayani, suna ambaton wasu majiyoyi daga cikin jami’an gwamnatin Amurka.
Sai dai har zuwa yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatocin Isra’ila ko Amurka da ke tabbatar da wannan rahoto.
A nata ɓangaren, Pakistan wadda ke da kyakkyawar alaƙa da Iran da kuma Amurka – ta nuna aniyarta ta taka rawar gani wajen sasanta rikicin da ke tsakanin ɓangarorin domin tabbatar da zaman lafiya a yankin.
Karanta: Iran Ta Kai Sabbin Hare-Hare Kan Cibiyoyin Soji Da Na Nukiliyar Isra’ila
