Iran Ta Kai Sabbin Hare-Hare Kan Cibiyoyin Soji Da Na Nukiliyar Isra’ila

Iran ta sanar da kai wasu sabbin hare-hare kan cibiyoyin soji da kuma wuraren masana’antu da ke da alaƙa da shirin makaman nukiliyar Isra’ila.

A cikin wata sanarwa da Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta fitar, ta ce hare-haren sun nufi muhimman wuraren soji da cibiyoyin fasaha da ake zargin suna da alaƙa da shirye-shiryen makaman nukiliya na Isra’ila.

Rahotanni daga kafofin labarai sun bayyana cewa Iran ta yi amfani da jirage marasa matuƙa (drones) da kuma makamai masu linzami wajen kai wannan hari, lamarin da ya ƙara tayar da hankali a yankin Gabas ta Tsakiya.

A ɓangaren Isra’ila kuwa, rundunar sojin ƙasar ta sanar cewa ta gano sabon harin makamai masu linzami da aka harba daga Iran, inda ta ce ana ci gaba da bibiyar lamarin tare da ɗaukar matakan kariya.

Harin na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin da ke tsakanin ƙasashen biyu ke ƙara tsananta, abin da ke janyo fargaba kan yiwuwar ƙarin tashin hankali a yankin.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.
Exit mobile version