INEC ta canza ranakun zaben 2027 a Najeriya

Independent National Electoral Commission (INEC) ta sanar da sabbin ranakun gudanar da zaben shugaban kasa, gwamnonin jihohi da kuma na ’yan majalisun tarayya da na jihohi na shekarar 2027.

Sauyin ya zo ne makonni biyu bayan hukumar ta fitar da jadawalin farko, wanda ya fuskanci suka daga bangarori daban-daban, musamman saboda yiwuwar ranakun su fada cikin watan azumin Ramadan na shekarar 2027.

Sakamakon haka, majalisar dokokin kasar ta yi gyara ga dokar zabe dangane da mafi karancin lokacin da ya kamata a sanar da ranar gudanar da zabe.

A jadawalin farko, INEC ta sanya ranar 20 ga watan Fabrairu 2027 domin zaben shugaban kasa da na ’yan majalisar dokokin tarayya, yayin da ta ware ranar 6 ga watan Maris 2027 domin zaben gwamnonin jihohi da na ’yan majalisun jihohi.

Sai dai a cikin sanarwar da ta fitar ranar Alhamis, 26 ga watan Fabrairu 2025, mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin wayar da kan masu kada kuri’a, Mohammed Kudu Haruna, hukumar ta bayyana cewa bayan gyaran dokar zabe ta 2022 da kuma amincewa da sabuwar dokar zabe ta 2026, an yi sauye-sauye ga jadawalin shirye-shiryen zabe domin ya dace da tsarin sabuwar dokar.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.
Exit mobile version