Hukumar Shige da Fice ta ƙasar Amurka (ICE) ta kama tsohon Ministan Kuɗin Ghana, Ken Ofori-Atta, sakamakon matsaloli da suka shafi bizar shigarsa ƙasar.
Lauyoyinsa daga Ghana, wato Minkah-Premo da Osei-Bonsu, Bruce-Cathline da Abokan Huldarsu (MPOBB), sun bayyana hakan a wata sanarwa da suka fitar ranar Laraba. Sun ce Ofori-Atta na bayar da cikakken haɗin kai ga hukumomin Amurka, yayin da tawagar lauyoyinsa da ke Amurka ke aiki tuƙuru domin tabbatar da sakin sa.
Sanarwar ta ƙara da cewa tsohon ministan ya miƙa takardar neman a gyara masa bizar zama, domin ba shi damar ci gaba da kasancewa a Amurka bayan karewar wa’adin bizar da yake da ita.
A Ghana kuwa, Ken Ofori-Atta na fuskantar tuhume-tuhume har guda 78 da suka haɗa da cin hanci da rashawa da kuma shirin aikata zamba a harkokin sayen kaya, lamarin da ake zargin ya jawo wa gwamnatin ƙasar asarar kuɗi masu yawa.
Ana zargin tsohon ministan da yin amfani da muƙaminsa wajen amincewa da biyan kamfanin Strategic Mobilisation Ghana Limited (SML) fiye da dala miliyan ɗaya, ba tare da sahihin hujjar ayyukan da aka gudanar ba.
Hukumomin Ghana sun nemi a miƙa shi zuwa ƙasar domin fuskantar shari’a, sai dai lauyoyinsa sun ƙalubalanci wannan buƙata a gaban doka.
Ghana da Amurka na da kyakkyawar alaƙar diflomasiyya, kuma a baya-bayan nan ƙasashen biyu sun yi aiki tare wajen mayar da ‘yan Afirka ta Yamma da ke fuskantar matsalolin shige da fice zuwa ƙasashensu na asali.
Rahotanni sun nuna cewa Ofori-Atta ya tafi Amurka ne domin neman magani kafin kama shi.
