Mutane da dama a kafafun yanar gizo suna ta cece kuce akan shigar da Zarah Ado Bayero yar gidan mai martaba sarkin Bici tayi a yayin gudanar da shugulgulan bikin ta da Yusuf Muhammadu Buhari a wannan makon.
A kafafun sada zumunta da wasu shafukan sun wallafa labarai kala kala akan wannan batun wasu na Allah wadai wasu na sa Albarka bisa shigan da Zarah tayi kayan nata yana nuna siraici kuma ya saba da da Al’adar kasar Hausa da kuma gidan da tafito na sarauta.
BBC Hausa sun wallafa labari akan wannan batu kamar haka – Hisbah: Ana ce-ce-ku-ce kan hotunan kwalliyar Zarah Bayero amaryar Yusuf Buhari