Kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon ta bayyana cewa ta kai hare-hare guda 63 kan Israel a ranar Lahadi, a wani sabon rikici da ke kara tsananta a yankin.
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta wallafa a shafinta na Telegram, Hezbollah ta ce ta yi amfani da makamai masu linzami, jirage marasa matuƙa (drones), da kuma manyan bindigogi wajen kai hare-haren kan sansanonin sojojin Isra’ila da wasu wurare a cikin Isra’ila da kuma kudancin Lebanon.
Rahotanni sun ce hare-haren na zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ila ta kara matsa lamba ta hanyar kaddamar da farmakin kasa a kudancin Lebanon, a wani mataki na mayar da martani ga barazanar da kungiyar ke yi.
Tun daga ranar 1 ga watan Maris, hare-haren da Isra’ila ke kaiwa a Lebanon sun yi sanadin mutuwar mutane sama da 1,029, yayin da mutane 2,786 suka jikkata, sannan sama da mutum miliyan guda suka rasa matsugunansu sakamakon rikicin da ke ƙara tsananta a yankin.
