Harin Amurka Ya Tarwatsa Sansanin Yan Bindiga a Sokoto

A yau ne rahotanni suka bayyana cewa an kai wasu hare-hare a sassan dazukan Ƙaramar Hukumar Tangaza da ke Jihar Sokoto. Rahotannin sun nuna cewa hare-haren sun shafi wuraren da ake zargin sansanonin ’yan bindiga ne, lamarin da ya sa wasu daga cikinsu suka tsere daga wuraren.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Tangaza, Isa Saleh Bashir, ya shaida cewa BBC Hausa cewa hare-haren sun faru ne a cikin daji, kuma wuraren da aka kai wa harin ana zargin sansanonin masu aikata ta’addanci ne. Daga cikin wuraren da abin ya shafa akwai wani ƙauye mai suna Tandami.

Har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, babu cikakken bayani kan asarar rayuka ko dukiyar da abin ya shafa, yayin da hukumomin tsaro ke ci gaba da sa ido kan lamarin.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.
Exit mobile version