Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta riga ta bai wa sama da ’yan Nijeriya miliyan 34 masu rauni tallafin kuɗi a ƙarƙashin shirin Conditional Cash Transfer, da nufin rage raɗaɗin matsin tattalin arziki da yaƙi da talauci a ƙasar.
Ministan Harkokin Jin-ƙai da Rage Talauci, Dokta Bernard Mohammed Doro, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a birnin Calabar na Jihar Cross River, yayin taron farko na National Council on Humanitarian Affairs and Poverty Reduction.
A cewarsa, shirin na nuna ƙwarin gwiwar gwamnatin Tarayya wajen fitar da miliyoyin ’yan Nijeriya daga talauci ta hanyar shirye-shiryen tallafi masu tsari, haɗin gwiwa, da kuma amfani da sahihan bayanai.
Ministan ya ƙara da cewa gwamnati ta sanya burin kai adadin masu cin gajiyar shirin zuwa miliyan 50 kafin ƙarshen shekarar nan, yana mai jaddada cewa kariyar jin-ƙai na daga cikin muhimman ginshiƙan manufofin rage talauci na gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
