Gwamnatin Tarayya da Gwamnonin APC Sun Bai wa Yan Kasuwar Singa Tallafin Naira Biliyan 8

Gwamnatin Najeriya ta sanar da bayar da tallafin kudi na naira biliyan 5 ga yan kasuwar Singa domin rage radadin asarar da suka yi sakamakon mummunar gobarar da ta lalata kasuwar.

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ne ya jagoranci wata tawaga zuwa Kano State, bisa umarnin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, domin jajanta wa wadanda ibtila’in gobarar ya shafa.

Da yake jawabi a gaban dandazon ƴan kasuwa, Shettima ya mika sakon jaje tare da sanar da tallafin naira biliyan 5 daga gwamnatin tarayya.

Hakazalika, ya bayyana cewa gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) guda 29 sun kara bayar da tallafin naira biliyan 3 ga wadanda asarar ta shafa.

A cewarsa, za a mika jimillar kuɗin naira biliyan 8 ga gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, domin kafa kwamiti da zai kula da yadda za a raba tallafin ga yan kasuwar.

Shettima ya kuma jaddada cewa Kano ita ce cibiyar kasuwanci a Arewacin Najeriya, don haka akwai bukatar hadin kai domin tallafa wa al’umma da kuma rage musu radadin wannan ibtila’i.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.
Exit mobile version