Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmad Aliyu, ya ƙaddamar da aikin sake gina babbar kasuwar jihar, wadda gobara ta lalata kimanin shekaru biyar da suka gabata.
A yayin ƙaddamar da aikin, gwamnan ya bayyana takaicinsa kan yadda ya ce gwamnatin da ta gabata ta kasa ɗaukar matakin sake gina kasuwar, inda maimakon haka ta jinginar da wani ɓangare na filin kasuwar ga wani banki.
Gwamna Ahmad Aliyu ya jaddada cewa kasuwar na taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tattalin arzikin jihar, don haka bai dace a bar ta cikin halin wofi da lalacewa ba.
Ya tuna cewa a watan Janairun 2021 ne babbar kasuwar Sokoto ta fuskanci mummunar gobara, lamarin da ya jefa ƴan kasuwa da dama cikin mawuyacin hali, yayin da wasu suka tilasta koma wa wasu kasuwanni domin ci gaba da sana’arsu.
“Da zarar gwamnatinmu ta karɓi ragamar mulki, mun kafa kwamitin bincike. Bayan dogon nazari, gwamnati ta yanke shawarar biyan kuɗin jinginar, kuma zuwa yanzu mun kammala biyan bashin, kasuwar ta kuma dawo hannunmu,” in ji gwamnan.
