Gwamnatin mulkin soji ta Burkina Faso ta sanar da rushe dukkan jam’iyyun siyasa da ƙungiyoyin siyasa a faɗin ƙasar, tare da miƙa dukiyoyinsu zuwa hannun gwamnati.
Rahoton kafar yaɗa labaran gwamnati ta RTB TV ya ce tun a shekarar 2022 ne aka dakatar da ayyukan jam’iyyun, kuma sabon matakin ya zama tabbatar da rushewarsu gaba ɗaya a hukumance.
An amince da dokar rushe jam’iyyun ne a yayin zaman majalisar zartarwa ta ƙasa, wanda shugaban mulkin sojin Burkina Faso, Kyaftin Ibrahim Traoré, ya jagoranta.
Mai magana da yawun gwamnatin ƙasar, Pingdwende Gilbert Ouédraogo, ya bayyana cewa an ɗauki matakin ne bayan nazarin rahoton bincike da aka gudanar domin sake fasalin da inganta tsarin gudanar da gwamnati, kamar yadda shafin labarai mai zaman kansa Lefaso.net ya ruwaito.
Kafin juyin mulkin da ya faru a watan Satumba na shekarar 2022, Burkina Faso na da jam’iyyun siyasa kusan 100, inda guda 15 daga cikinsu ke da wakilci a majalisar dokokin ƙasar.
