Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ba ta taba goyon bayan muzgunawa Kiristoci ko nuna wariyar addini ba, biyo bayan rahoton bincike da Majalisar Wakilan Amurka ta fitar kan zargin cin zarafi da kashe-kashen Kiristoci a kasar.
Gwamnatin ta ce duk da cewa akwai kalubalen tsaro a wasu yankuna, matsalolin na da alaka ne da ta’addanci, fashi da makami da rikice-rikicen al’umma, ba wai saboda bambancin addini ba.
Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata. Ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya tabbatar da ‘yancin addini da ibada ga kowane ɗan ƙasa, kuma gwamnati na da ƙudurin kare wadannan hakkoki tare da tabbatar da adalci ga kowa.
Ministan ya kara da cewa gwamnati ta kara karfafa hadin gwiwar jami’an tsaro a yankunan da matsalar ta fi kamari, tare da fadada yaki da ta’addanci, rusa hanyoyin masu garkuwa da mutane da kuma cafke manyan masu aikata laifuka.
Haka kuma, sanarwar ta nuna cewa an inganta haɗin kai tsakanin hukumomi domin saurin ɗaukar mataki, musamman a yankunan karkara da ke da rauni.
Gwamnatin ta kuma jaddada muhimmancin dangantakar Najeriya da Amurka, tana mai cewa kasar na maraba da tattaunawa da hadin kai bisa mutunta juna da ikon kowace kasa.
Ta kara da cewa za ta ci gaba da aiki da abokan huldar kasa da kasa ta hanyar diflomasiyya, yayin da take bai wa fifiko ga babban alhakin kare rayuka da dukiyoyin dukkan ‘yan kasa.
A ranar Litinin ne ‘yan Majalisar Wakilan Amurka suka mika rahotonsu ga Shugaban Amurka, Donald Trump, bayan kammala bincike kan zargin cin zarafi da muzgunawa Kiristoci a Najeriya.
