Gwamnatin Najeriya Ta Fara Kwaso ’Yan Kasarta Daga Iran

Gwamnatin Najeriya ta fara daukar matakin kwaso ’yan kasarta da ke zaune a Iran wadanda suka nemi a dawo da su gida, inda ake raka su zuwa kan iyakar kasar Armeniya domin tabbatar da tsaron lafiyarsu yayin da ake ci gaba da tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya.

Shugabar Hukumar ’Yan Najeriya Mazauna Kasashen Waje, Abike Dabiri-Erewa, ta bayyana hakan a wani sako da ta wallafa a shafinta na X a ranar Talata.

Ta kuma tabbatar da cewa zuwa yanzu babu wani dan Najeriya da rikicin da ke faruwa a Iran ya shafa. Ta ce jami’an ofishin jakadancin Najeriya suna kan iyakar Iran da Armenia domin karɓa da kuma taimakawa ’yan Najeriya da ke son barin ƙasar.

Dangane da jigilar su ta jiragen sama zuwa gida kuwa, Dabiri-Erewa ta bayyana cewa a halin yanzu sararin samaniyar yankin ba shi da cikakken tsaro saboda rikicin, amma gwamnatin tarayya na ci gaba da shirye-shiryen kwaso su.

Ta ce an samu jirgin da ya taso daga United Arab Emirates zuwa Lagos kwanaki biyu da suka gabata kafin wani sabon hari ya sa aka rufe sararin samaniyar wasu sassan yankin.

Shugabar ta kara da cewa da zarar an bude sararin samaniyar, tawagar gwamnatin tarayya da ta kunshi jami’ai daga ma’aikatu daban-daban za ta fara aikin kwaso ’yan Najeriya.

Wannan mataki na zuwa ne bayan karuwar rikicin da ya fara a ranar 28 ga watan Fabrairu, bayan wani hari da United States da Israel suka kai kan Iran.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.
Exit mobile version