Gwamnan Zamfara ya bayyana dalilin komawarsa APC

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa rikicin cikin gida da kuma matsalolin shari’a da suka dabaibaye tsohuwar jam’iyyarsa, Peoples Democratic Party (PDP), su ne suka sa ya yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar zuwa All Progressives Congress (APC).

A ranar Litinin ne gwamnan ya sanar da sauya shekarsa a hukumance bayan wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a gidan gwamnatin jihar da ke Gusau.

A wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa matakin da gwamnan ya dauka na komawa APC ya zama wajibi domin kare muradun al’ummar Zamfara.

Sanarwar ta kara da cewa gwamnan ya dauki wannan mataki ne bayan tuntuba da shawarwari da manyan masu ruwa da tsaki a jihar, musamman ganin irin matsalolin shari’a da jam’iyyar PDP ke fuskanta a halin yanzu.

A cewar gwamnan, ya yi iya kokarinsa wajen sasanta rikicin da ke tsakanin bangarorin jam’iyyar domin samar da hadin kai da kuma tabbatar da cewa jam’iyyar za ta iya tsayar da yan takara a zabukan da ke tafe.

Sai dai ya ce duk kokarin da aka yi na sulhu bai haifar da sakamako ba, lamarin da ya kai ga yawaitar shari’o’i da ka iya yin tasiri ga ƴan siyasa da za su nemi takara a zaɓen shekarar 2027.

Ficewar Dauda Lawal daga PDP na zuwa ne mako guda bayan sauya shekar wani gwamnan daga Adamawa zuwa jam’iyyar APC, lamarin da ke kara sauya taswirar siyasar Najeriya.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.
Exit mobile version