Gwamnan Sokoto Ya Umarci A Gaggauta Biyan Albashi Gabanin Azumin Ramadan

Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya ba da umarnin a fara biyan ma’aikatan jihar albashin watan Fabrairu nan take, domin saukaka musu shirye-shiryen karbar watan azumin Ramadan mai zuwa.

An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a na ofishin gwamnan, Abubakar Bawa, ya fitar a yau Alhamis.

Sanarwar ta ce umarnin ya shafi ma’aikatan gwamnatin jiha, ma’aikatan kananan hukumomi, ma’aikatan Hukumar Ilimin Ƙananan Hukumomi, da kuma tsofaffin ma’aikata masu karɓar fansho a faɗin jihar.

Haka kuma, an bayyana cewa za a fara biyan albashin daga ranar Juma’a, 13 ga watan Fabrairu.

Ana sa ran al’ummar Musulmi a fadin duniya za su fara azumin watan Ramadan a ranar 18 ko 19 ga watan Fabrairu na wannan shekara.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.
Exit mobile version