Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya bai wa kowane maniyyaci daga Jihar Kano tallafin naira dubu ɗari biyar domin cika kuɗin Aikin Hajji.
Wannan na zuwa ne bayan Hukumar Alhazan Nijeriya NAHCON ta buƙaci kowane maniyyaci wanda ya biya kafin alƙalami a baya ya cika aƙalla naira miliyan 1.9.
A sanarwar da ya fitar a shafinsa na X, gwamnan na Kano ya ce a yanzu kowane maniyyaci daga Kano naira miliyan 1.4 zai bayar ga hukumar alhazan maimakon miliyan 1.9.
“Bayan ƙarin miliyan 1.9 na kuɗin Aikin Hajji da Hukumar Alhazan Nijeriya ta yi, na amince a bai wa kowane maniyyaci daga Kano N500,000 domin tafiya Saudiyya.
“Dangane da haka, maniyyatan da suka biya kafin alƙalami a baya na miliyan N4.7 da miliyan N4.5 ga hukumar alhazan jihar a halin yanzu za su cika miliyan N1.4 maimakon miliyan N1.9,” inji gwamnan.
Tun da farko dai Hukumar Alhazan Nijeriyar NAHCON ta ƙara farashin kujerar Aikin Hajjin bana da miliyan N1,918,032.91, inda ta bai wa maniyyata wa’adin zuwa 28 ga watan Maris ɗin 2024 su biya cikon kuɗin.
Hukumar ta NAHCON ta ce an samu wannan ƙarin ne sakamakon ƙaruwar farashin dala a Nijeriya.
Sai dai hakan ya jawo martani da dama daga faɗin ƙasar inda aka yi ta kira ga gwamnatin ƙasar ta sassauta.