Gobara ta barke a kasuwar Muda lawan dake cikin garin Bauchi a yau Alhamis.
Rahotanni da suke shigo mana daga jihar Bauchi sun nuna cewar daya daga cikin manyan kasuwannin jihar Bauchi ta Muda Lawal ta kama da wuta.
Bayanai sun nuna shaguna da yawa sun kone. Ya zuwa yanzu ba a kai ga gano musabbabin afkuwar gobarar ba da kuma irin asarar da aka tafka.
Zamu sabunta shafin domin kawo muku asalin me ya faru nan gaba.