Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaben 2023, Nasiru Yusuf Gawuna, ya sanar da ajiye mukaminsa na Shugaban Hukumar Gudanarwar Bankin Bayar da Lamunin Gidaje na Najeriya.
A wata sanarwa da ya fitar, Gawuna ya ce ajiye mukamin zai fara aiki ne daga Talata, 31 ga Maris, 2026.
Ya bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne domin bin umarnin shugaban kasa wanda ya bukaci duk masu rike da mukaman siyasa da ke da niyyar tsayawa takara su sauka daga mukamansu domin bin dokar zabe.
Gawuna ya kuma nuna godiyarsa ga Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu bisa amincewar da ya yi masa wajen naɗa shi shugaban hukumar gudanarwar bankin.
