Garo Ya Jinjinawa Hisbah Kan Gudummawar Kano

Mataimakin gwamnan jihar Kano, Alhaji Murtala Sule Garo, ya yabawa hukumar Hisbah bisa irin gudummawar da take bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban jihar Kano.

Ya bayyana cewa ayyukan hukumar sun taimaka matuka wajen karfafa tarbiyya da kyawawan dabi’u a tsakanin al’umma.

Garo ya yi wannan jawabi ne yayin da ya karbi bakuncin shugabannin hukumar Hisbah da suka kai masa ziyarar girmamawa a ofishinsa.

A yayin ganawar, ya nuna jin dadinsa kan yadda hukumar ke aiki tare da gwamnati domin tabbatar da cigaban jihar.

Har ila yau, mataimakin gwamnan ya tabbatar wa shugabannin hukumar cewa zai tattauna da Gwamna Abba Kabir Yusuf domin a duba bukatun da suka gabatar, tare da nemo hanyoyin da za a bi wajen tallafa musu domin su ci gaba da gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

Exit mobile version