Dan jihar Borno da Yar Zamfara sun lashe Musabakar Al-Qur’ani da kyautar N6,000,000

Dan jihar Borno ya lashe gasar izu 60 ta karatun Al Kur’ani mai tsarki ta ƙasa Najeriya da aka kammala a jihar Bauchi.

Baba Sanyinna Goni Mukatar ya karɓi kyautar naira miliyan uku N3,000,000

Yar jihar Zamfara  Haulatu Aminu Ishaq ce ta lashe gasar izu 60 ɓangaren mata. Ita ma ta lashe kyautar naira miliyan uku N3,000,000.

Wannan ne karo na 36 da ake gudanar da gasar da Jami’ar Usman Danfodio da ke Sokoto ke jagoranta.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.
Exit mobile version