Bayan Aure: Sabbin Hotunan Rahama Sadau Sun Haddasa Cece-kuce a Kafafen Sada Zumunta

Fitacciyar jarumar Kannywood da Nollywood, Rahama Sadau, wadda akayi aurenta a watan Agusta 2025 da mijinta Ibrahim Garba, ta sake jawo hankalin jama’a bayan ta saki wasu sabbin hotuna a shafukan sada zumunta a yau juma’a inda tace:

Jumu’ah Mubarak! 🤲🏽✨🤎🤍 May we be blessed with inner peace, mercy, and countless blessings. Ameen 🤲🏻🤎
#JumaatMubarak #AmaryaMaiCApacity


Hotunan da jarumar ta wallafa sun yi kyau sosai inda suka dauki hankalin masoyanta da mabiyanta, musamman ganin cewa sun zo ne a cikin watanni biyu kacal bayan auren nata.

Wasu daga cikin masoyan sun bayyana jin dadinsu da hotunan, suna yaba mata kan kyan shigar da ta yi da kuma salon da ya nuna al’adun Hausawa da zamani. Sai dai kuma akwai wasu da suka yi ta cece-kuce kan cewar Amaryar Bogice ita wasu kuma sukace ko ya dace da sabuwar matar aure ta fitar da irin wannan hotuna a kafafen sada zumunta.

Rahama Sadau dai ta shahara wajen kawo salo iri-iri a masana’antar Kannywood da Nollywood, inda ta riga tayi suna a Najeriya da kasashen waje. Bayan auren nata, da dama sun yi tsammanin za ta rage irin wallafe-wallafen da take yi na hotuna da yake jawo cece kuce, amma sabbin hotunan sun sake nuna cewa jarumar ba ta sauya salon nata ba.

Tun bayan da ta shiga harkar fim a 2013, Rahama ta kasance daya daga cikin fitattun jaruman Kannywood, sannan daga baya ta yi fice a Nollywood da ma Bollywood. A yanzu kuma, bayan auren nata, ta ci gaba da kasancewa cikin jerin jaruman da jama’a ke bibiyarsu a kullum a kafafen sada zumunta inda take da mabiya miliyan daya da rabi a facebook.

Masu sharhi na ganin wannan cece-kuce wani bangare ne na irin farin jinin da take da shi a kafafen sada zumunta, inda Rahama Sadau ta kasance daya daga cikin jaruman da suka fi shahara a Arewacin Najeriya.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.
Exit mobile version