Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai an ceto dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su a ƙauyen Kurmin Wali da ke Ƙaramar Hukumar Kajuru.
Gwamnan ya bayyana cewa yana bibiyar aikin jami’an tsaro kafaɗa da kafaɗa, tare da tabbatar da cewa gwamnati ta karkata dukkan ƙoƙarinta ne kan ceto mutanen da aka sace, ba tare da gajiya ba.
A ranar Lahadi ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari ƙauyen Kurmin Wali, inda rahotanni suka nuna cewa an sace fiye da mutane 170, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin firgici da ruɗani. Da farko, hukumomin tsaro da gwamnatin jihar sun musanta faruwar lamarin, sai dai daga baya suka tabbatar da shi, kodayake har yanzu ba a bayyana ainihin adadin mutanen da aka sace ba.
A hirarsa da BBC a Kaduna, Gwamna Uba Sani ya ce gwamnatinsa ba ta mayar da hankali kan ƙididdigar adadin waɗanda aka sace ba, illa dai aikin ceto su cikin gaggawa. Ya bayyana cewa mayar da batun tsaro siyasa ne ke janyo ruɗani.
“Mu a jihar Kaduna ba mu siyasantar da batun tsaro. Waɗanda suka mai da shi siyasa za su ji kunya,” in ji gwamnan.
Dangane da zargin rufa-rufa a farkon bayyanar labarin, Gwamna Uba Sani ya ce ya gamsu da yadda jami’an tsaro ke gudanar da aikinsu da gaskiya da haɗin kai, yana mai jaddada cewa suna aiki tukuru domin ganin an ceto mutanen da aka sace.
Ya ce ya riga ya zauna da manyan jami’an tsaro a matakin ƙasa, ciki har da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Malam Nuhu Ribadu; Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa; Darakta Janar na DSS; da Sufetan Ƴan Sandan Ƙasa, domin tabbatar da haɗin gwiwa cikin gaggawa wajen dawo da mutanen gida lafiya.
Gwamnan ya kuma bayyana karara cewa gwamnatinsa ba ta da shirin biyan kuɗin fansa, duk da cewa masu garkuwa da mutanen ba su tuntuɓi gwamnati ko bayyana abin da suke nema ba.
“Muna da tsari na rashin biyan kuɗin fansa, kuma ba za mu kauce masa ba,” in ji shi.
Ya yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da ba jami’an tsaro cikakken haɗin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai, yana mai jaddada cewa batun tsaro ba aikin gwamnati kaɗai ba ne.
“A matsayina na gwamna, ba zan kwanta ba, ba zan huta ba. Da yardar Allah, za mu tsaya tsayin daka har sai mun ga an dawo da kowa gida lafiya ba tare da wata matsala ba,” in ji Uba Sani.
A halin da ake ciki, ɗaya daga cikin waɗanda aka sace, Maigirma Shekarau, ya bayyana yadda ya samu damar tserewa daga hannun ‘yan bindigar. Ya ce suna cikin coci lokacin da harin ya faru, inda suka ji ihu kafin su ga ‘yan bindiga sun kewaye ƙauyen tare da tilasta musu shiga daji.
Ya ce a yayin tafiyar, an riƙa musu tambayoyi tare da duka, kafin daga bisani ya samu damar sulalewa a wani wuri da ake kira Sabon Gida, inda ya ɓoye tare da wata yarinya har ‘yan bindigar suka tafi.
Maigirma ya tabbatar da cewa an sace mutane da yawa, yana mai bayyana damuwar al’umma kan halin da sauran waɗanda aka tafi da su ke ciki, yayin da ake fatan samun nasarar ceto su cikin gaggawa.
