APC Ta Zabi Sabbin Shugabanninta

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta zabi sabbin shugabannin da za su jagoranci harkokin jam’iyyar na tsawon shekaru huɗu masu zuwa.

An bayyana sabbin shugabannin ne a yayin babban taron ƙasa na jam’iyyar da aka gudanar ranar Juma’a a birnin Abuja, inda wakilai daga sassa daban-daban na ƙasar suka halarta.

A yayin taron, jam’iyyar ta tabbatar da Farfesa Nentawe Yilwatda, wanda ke rike da mukamin shugaban riƙo a baya, a matsayin cikakken Shugaban Jam’iyyar na ƙasa. Haka kuma an tabbatar da Sanata Surajudeen Ajibola Basiru a matsayin Sakataren Jam’iyyar na ƙasa.

Rahotanni sun nuna cewa yawancin shugabannin da aka zaɓa sun samu mukamansu ne ta hanyar masalaha (consensus), wata hanya da jam’iyyar ta fi amfani da ita wajen cimma matsaya tsakanin ‘ya’yanta.

Jerin Sabbin Shugabannin APC

KARANTA: Manyan Jiga-Jigan APC Sun Hallara A Babban Taron Jam’iyya A Abuja

Ana sa ran sabbin shugabannin za su jagoranci jam’iyyar wajen tsara dabarun siyasa da shirye-shiryen da za su tunkari manyan zaɓuɓɓukan siyasa masu zuwa a Najeriya.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.
Exit mobile version