APC Ta Tantance Isa Pantami A Abuja

Tsohon ministan sadarwa, Isa Ali Pantami, ya halarci kwamitin tantance ‘yan takarar gwamna na All Progressives Congress a matsayin dan takarar gwamnan jihar Gombe State.

An gudanar da tantancewar ne a safiyar Asabar a Kaduna State Governor’s Lodge da ke Asokoro a Abuja, inda kwamitin APC na kasa ya karɓi Pantami domin tantance shi gabanin zaben fidda gwani na jam’iyyar.

Rahotanni sun bayyana cewa tantancewar na daga cikin shirye-shiryen jam’iyyar APC na zaben fidda gwani da ake sa ran gudanarwa cikin makwanni biyu masu zuwa.

Magoya bayan Pantami sun bayyana goyon bayansu ga tsohon ministan, tare da kira ga mabiyansa da su kasance cikin shiri domin matakin gaba na fafatawar siyasa.

Masu sharhi kan harkokin siyasa a jihar Gombe na ganin cewa shigar Pantami takarar gwamna na kara zafafa siyasar APC a jihar yayin da ake tunkarar zaben 2027.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

Exit mobile version