Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta ƙaryata rahotannin da ke yawo na cewa tana shirin sauya Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, a matsayin abokin takarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shekarar 2027.
Jam’iyyar ta bayyana cewa irin waɗannan rahotanni ba su da tushe balle makama, tana mai cewa tsantsar jita-jita ce da aka ƙirƙira domin haddasa ruɗani da tayar da rikici a harkokin siyasar ƙasar.
Wannan bayani ya fito ne cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na APC, Felix Morka, ya fitar, inda ya yi kira ga jama’a da su yi watsi da rahotannin marasa tushe.
A ƴan shekarun nan, an daɗe ana raɗe-raɗin cewa jam’iyyar mai mulki na iya sauya mataimakin shugaban ƙasa gabanin babban zaɓen shekarar 2027. Haɗin gwiwar Bola Tinubu da Kashim Shettima tun farko ya fuskanci suka daga wasu sassa na ƙasar, musamman kan batun addini, inda wasu ke ganin hakan ya saɓa da tsarin da aka saba na bambancin addini tsakanin shugaban ƙasa da mataimakinsa.
Sai dai a lokuta da dama, masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC sun jaddada cewa haɗin Tinubu da Shettima dabara ce ta siyasa da ta taimaka wajen samun nasara a zaɓen shekarar 2023.
Ana sa ran harkokin siyasa za su ƙara ɗaukar zafi a shekarar 2026, gabanin babban zaɓen ƙasar na 2027, inda ake hasashen Shugaba Tinubu zai sake tsayawa takara domin neman wa’adin shugabanci na biyu na tsawon shekaru huɗu.
