Ana zargin wani magidanci da sheke budurwar sa ta hanyar kisan gilla.

Masu bincike daga Sashen Binciken Laifuka ta kasar kenya waton DCI – Detectives from the Directorate of Criminal Investigations, sunyi ram da wani magidanci mai shekaru 38 a duniya da suke zargin yayi kisan gilla da budurwasa.

Wanda ake zargin dai sunansa Evans Karani da ake tuhumar sa akan kashe wata budurwa yar shekaru 25 a duniya mai suna Catherine Nyokabi da take uguwar Witeithie dake cikin Juja a jihar Kiambu a kasan Kenya.

Babban Jami’in bincike na karamar hukuma Juja main suna Richard Mwaura, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Juma’a, 16 ga Afrilu, ya ce wanda ake zargin ya yi kokarin jefar da gawar Nyokabi a ranar Laraba motar da sa ta tsaya a cikin laka ya riketa,

Mota mai dauke da gawar Nyokabi

A yayin da yake kokarin tafiya domin jefar da gawar Nyokabi a cikin motarsa, motar tasa ta makale a laka a kan hanyar Bob Harris a Juja, hakan yasa ya yanke wa kansa nima arcewa ya bar motar da gawar Nyokabi a bayan motar sa, inji Sashen Binciken Laifuka.

‘Yan sanda, wadanda suka isa wurin bayan wani rahoto da mazauna yankin suka bayar, sunyi bincike sun tabbatar da mallakar motar daga Humar kula da sufurin da tsaro na ababen hawa da kuma rijistan ababen hawa na kasa.

Sakamakon haka ne, aka fara farautar magidancin mai suna Karani ta hanyar wata rundunar tsaro da ta kunshi ‘yan sanda, jami’an DCI da jami’in hukumar binciken laifuka da hukumar leken asiri (CRIB)

A safiyar ranar Juma’a, 16 ga Afrilu, ‘yan sanda, ta hanyar siginar waya suka bibiye magidancin zuwa gidansa da yake haya a yankin Githurai Kimbo, inda suka samu nasarar cafke.

Hukumomin bincike sun ce gawar matashiya Nyokabi an kona ta ce ta hanyar amfani da sinadari lalatacce.

Hukumomi masu bincike sun ce wanda ake zargin ya furta cewa ya kashe Marigayiyar mai suna Nyokabi shidin ma’aikacin otal ne a Kahawa Wendani, sakamakon wani mummunan rikici, wanda suka shiga cikin makonni biyu da suka gabata.

Karani wanda ake zargin yace yana da aure kuma shi da marigayiyan mai suna Nyakabi masoyane na sirri wanda hakan ya shaidawa ‘yan sanda.

Mahaifin marigayiyar, mai suna Gitonga Njogu, ya shaida wa gidan jarida mai suna The Standard cewa rahotannin farko sun nuna ’yarsa, ta farko da aka haifa a cikin’ ya’yan sa hudu, ta mutu a hatsarin mota akan hanya.

“A Shafin sada zumunta na Facebook, wasu mutane suna ikirarin cewa ‘yata ta mutu a hatsarin mota a Juja. Duk da haka, lokacin da muka ga gawarta a dakin ajiyar gawawwakin birni, sai muka damu hankalin mu ya tashi da Raunin da muka gani a fili ya nuna dalilin mutuwar marigayiyar Nyokabi ba hatsarin mota bane kamar yadda aka zargi, “in ji Njogu.

“Yar tawa (Nyokabi) mai kwazo ce, mai fara’a da son mutane. Makomarta na da kyau, ”in ji mahaifin marigayiyar yayin da hawaye yake kwararowa daga idanun sa.

Tsohon marigayiya Nyokabi, yace a da, ta gabatar da wanda ake zargin Karani a matsayin manemin ta.

“Na san Nyokabi da Karani su masoya ne. Kamar dai a kowace soyayya akwai bambance-bambance da sauran rikice rikice wanda ake samu kuma ina taimaka musu wurin sulhu. Makonni biyu da suka gabata, ɗiyata Nyokabi ta ce ita da Karani sun rabu. Na ce mata, ba komai; bai kamata ta kasance acikin taraiyyan da babu farin ciki aciki ba. Wannan shi ne karo na karshe da na ji labarin wanda ake zargin. ”

Za a gurfanar da Karani a ranar Litinin, 19 ga Afrilu, hakan zai ba dama da masu bincike su tsare shi har tsawon lokacin da zaa kammala bincike.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.
Ta
Linda Ikeji
Exit mobile version