An ƙara tsaurara matakan tsaro a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar, bayan da aka shafe kusan awa biyu ana harbe-harben bindiga a filin jirgin saman birnin.
Ya zuwa yanzu, gwamnatin mulkin sojin ƙasar ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba. Sai dai ana yaɗa jita-jitar cewa ko dai an yi yunƙurin juyin mulki ne ko kuma wani samame da aka kai kan masu ɗauke da makamai.
Mazauna unguwannin da ke kusa da filin jirgin sun shaida wa manema labarai cewa sun farka ne sakamakon ƙara mai ƙarfi, inda daga bisani aka shafe lokaci mai tsawo ana jin karar harbe-harbe.
Har zuwa yanzu, babu rahoton samun asarar rai ko jikkata, haka kuma ba a bayar da rahoton lalacewar gine-gine ko dukiya ba.
Rahotanni sun nuna cewa filin jirgin saman Yamai na ɗauke da shalkwatar rundunar sojojin haɗin gwiwa ta ƙasashen Nijar, Mali da Burkina Faso, waɗanda ke yaƙi da ƙungiyoyin da ke ikirarin jihadi.
