Fadar Mai Alfarma Sa’ad Abubakar III, Sarkin Musulmin Najeriya, ta sanar da cewa Musulman kasar za su fara azumin watan Ramadan a ranar Laraba, 18 ga Fabrairu, 2026.
Sanarwar ta tabbatar da shigar watan Ramadan mai alfarma, wanda Musulmi a fadin duniya ke gudanar da ibadar azumi daya daga cikin ginshikan addinin Musulunci guda biyar.
A wata sanarwa da fadar Sarkin Musulmi ta fitar a daren Talata, an bayyana cewa an samu sahihan rahotannin ganin watan a wurare daban daban na kasar, wanda ya sa aka ayyana ranar Laraba, 18 ga Fabrairu, a matsayin ranar 1 ga watan Ramadan na bana.
Sarkin Musulmin ya buƙaci al’umma su himmatu wajen ibada tare da sanya kasar cikin addu’o’in zaman lafiya, hadin kai, da kwanciyar hankali.
A baya, hukumomin Saudiyya su ma sun sanar da ganin watan, tare da umartar Musulmi su fara azumi a ranar Laraba.
Watan Ramadan lokaci ne da Musulmi ke kara kaimi wajen ibada, kyautatawa juna, da taimaka wa mabukata domin neman lada da kusanci ga Allah. Haka kuma lokaci ne da ake ninka ladan ayyukan alheri da ibadu.
