Shafin BBC Hausa sun rawaito cewa Hukumar yaƙi da ta’amali da migayun ƙwayoyi wato NDLEA, ta kama wata mata ƴar ƙasar Chadi ƙunshe da hodar ibilis a al’aurarta a tashar jirgin sama da ke Abuja.
An cafke matar ne lokacin da taƙe ƙoƙarin hawa jirgin Ethiopia da zai dangana da ita Addis Ababa zuwa Italiya ɗauke da gram 234.5 na hodar.
Tarmadji wacce ke sana’ar gyaran gashi a Italiya, tun 2016 kafin ta dawo ƙasar ta Libya an cafke ta ne a lokacin da ake binciken fasinjoji a wajen hawa jirgi.
Sanarwar da kakakin NDLEA ya fitar, Femi Babafemi, ta ce ana kan bincikerta kuma bayanan da suka samu kawo yanzu na cewa wani mutum ne ɗan Italiya ya bata ƙunshin hodar a Legas.
Ta kuma shaida cewa mutumin ya bata ƙullin hodar ibilis 50 ta haɗiye amma ta nuna masa ba za ta iya ba, don haka sai ta yanke hukunci cusa ƙulli 18 a al’aurarta.
Tarmadji ta ce, ta zo Najeriya ne domin ta samu kuɗin da za ta biya haya da shagon da take gyaran gashi saboda rayuwa ta yi wahala a Italiya saboda annobar korona.
Ta kuma ce Euro dubu 10 za a biyata idan ta samu wucewa da hodar zuwa Italiya..