Yan sandan Jihar Katsina sun tabbatar wa DW rasuwar Sheikh Yahaya Malam Masussuka, wanda wasu da ake zargin ’yan bindiga ne suka harbe a ƙofar gidansa da ke garin Dutsinma.
Rahotanni sun nuna cewa maharan, waɗanda ake zargin suna amfani da babura, sun kai masa harin ne a ƙofar gidansa.
Har zuwa lokacin da aka fitar da wannan rahoto, ba a bayyana ƙarin bayani kan dalilin harin ko waɗanda suka aikata shi ba.
Ku kasance da Hausa360 — Ingantaccen shafi don samun sahihan labarai
