Akalla mutane 25 ne suka rasa rayukansu a wasu hare-hare guda biyu da ake zargin mayakan Boko Haram ne suka kai a jihar Adamawa da ke arewacin Najeriya, kamar yadda wasu mazauna yankin suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP a ranar Alhamis.
Hare-haren sun faru ne a garuruwan Madagali da Hong, wadanda ke kusa da iyakar kasar Kamaru. An danganta su da kungiyar Boko Haram, wadda ta shafe shekaru tana kai hare-hare a yankin tun bayan fara tayar da ƙayar baya a 2009.
Wani jami’in karamar hukumar Madagali, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa wasu ‘yan bindiga da ake zaton ‘yan Boko Haram ne, sun shiga kasuwa a kan babura inda suka buɗe wuta kan jama’a, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum 21.
Ya kara da cewa ana ci gaba da bincike domin gano wasu gawawwaki, domin akwai yiwuwar wasu sun mutu a cikin daji sakamakon raunukan harbin bindiga yayin da suke ƙoƙarin tserewa.
Rahotanni sun ce maharan sun kuma kwashe kayayyaki daga kasuwar, ciki har da abinci da babura.
A wani hari daban a garin Hong, mutane hudu sun mutu, ciki har da sojoji uku, kamar yadda wani mazaunin yankin mai suna Ezekiel Musa ya bayyana.
