Amurka ta umarci ma’aikatanta su bar kasashen Gabas ta Tsakiya

Gwamnatin United States ta bukaci wasu daga cikin kananan ma’aikatan jakadancinta da ayyukansu ba su da muhimmanci su gaggauta ficewa daga wasu kasashen yankin Gabas ta Tsakiya, sakamakon karin damuwa da ake ciki kan matsalar tsaro a yankin.

Rahotanni sun bayyana cewa matakin ya shafi kasashe da dama, ciki har da Kuwait, Iraq, United Arab Emirates, Bahrain da kuma Jordan. Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar karin tashin hankali da rashin tabbas a yankin.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta kuma shawarci ‘yan kasarta da ke zaune ko ziyara a yankin da su bi umarnin hukumomi tare da ci gaba da bibiyar kafofin watsa labarai na cikin gida domin sanin halin da ake ciki.

Tun da farko dai ofishin jakadancin Amurka da ke Kuwait ya sanar da rufe kofofinsa na wani dan lokaci, yana mai cewa matakin ya biyo bayan karin tsanantar lamuran tsaro a yankin Gabas ta Tsakiya.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.
Exit mobile version