Alison ta fassara Kundin Karatun koronabairos zuwa harshen Hausa

Babban shafin karatun kyauta na Kasar Ireland wato ALISON Free Online Courses & Online Learning ya fassara karatu akan ilimin Koronabairos zuwa harshen Hausa.

Shafin ya yi hakan ne dan ya bawa kasashen Afrika damar samun cikakken ilimi da kuma sanin hakikanin mece ce cutar Koronabairos a cewar shugar shugan Alison Mike Feerick a wani sako na musamman da ya turawa shugan Hausa360 yace.

“Ga mazauna Nahiyar Afrika masu bukatar fahimtar duk wani muhimmin bayani game da cutar Koronabairos, mun kaddamar da shahararren kundinmu na kyauta kan ilimin Koronabairos cikin manyan harsunan guda 13 da ake magana da su a nahiyar Afrika wanda ya hada da harshen Hausa.”

“Kundin ya kunshi bayani akan asalin cutar Koronabairos da sababbin bayanai game da cutar da yadda ake gane alamomin cutar da kuma abubuwan da za a yi domin hana yaduwar cutar.”

Ya kuma kara da cewa “Ku tallatawa ‘yan uwa da abokai da al’umma baki daya wannan kundi ta kafofin yada zumunta da WhatsApp da sakon Email da duk wasu hanyoyi domin taimaka mana wajen wayar da kan jama’a da kuma kiyaye yaduwar cutar.”

Sannan ya kukke sakon sa da cewa Manyan harsunan Afrika da muke da fassararsu su sun hada da;
Shona da Swahili da Sesotho ta Kudu da Somali da Hausa da Xhosa da Portugese da Yoruba da Igbo da French da isiZulu da kuma Afrikaans.

Muna kokarin samar da fassarar harshen Larabci da na Amharic. Ba da dadewa ba za a iya samunsu akan shafin namu.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.
Exit mobile version