Wani Matashi mai suna Nasiru Damanga dan uguwan RAN kan titin ajiya adamu dake cikin garin Bauchi yayi sanadiyyar mutuwar abokan sa biyu har lahira ranar Alhamis da ta gabata.
Matashin Mai suna HARISU YADO ya mutu ne sanadiyyar abokan sa da suka zo satan mashi, bayan sunyi ido biyu da barayin mashin nasa, sai daya daga cikin barayin wanda ake zaton Nasiru Damanga ya chaka masa wuka a kirji wanda yayi sanadiyyar mutuwar sa har lahira.
Wanda hakan yaja hankalin al’uman anguwa, suka samu nasarar kama daya acikin bayarin su biyar mai suna Habu Madara, ganin ta’asan da barayin suka aikata yasa aka lakada mishi duka, washe gari da assuba ranan juma’a shi kuma ya mutu.
Acewar daya dacikin yan unguwan Na Ajiya Adamu mai suna Babangida ya shaida mana cewa iyayen yaran dukkan su abokan juna ne, tare suke komai.
Yakara da cewa maganar yana wurin hukumar yan sanda domin bincike da kuma sanin asalin me ya faru.
In baku mance ba a waccan satin ne a cikin garin bauchin aka samu gawar wani saurayi bayan masu garkuwa sun karba kudi kuma suka kashe shi har lahira.